<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>249</hymn_number>
<title>Ya Yesu Mai Ceto, Ka Ba Ni Sabon Rai LW249</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu Mai Ceto, ka ba ni sabon rai,
 Ka tsarkake ni da jininka, in ji, in bi sosai.

[V2]
 KORUS
 Ka ba ni sabon rai, a cikin zuciyata.
 Ka sauko nan da ikonka, ka ba ni sabon rai !

[V3]
 Ya Ruhu Mai Tsarki, farkad da ni yanzu
 Daga nauyi, barci, ragwanci, ka wartsakad da ni.
 Korus

[V4]
 3) Uba, ina roƙonka ka ba ni ƙishirwa
 Ka shayar-da ni da ruwa mai rai, ka amsa kukana.
 Korus

[V5]
 4) Yesu, Ruhu, Uba, na girmama ka yau.
 Ka sauko nan da ikonka, na ba ka zuciyata.
 Korus

[V6]
 5) Sai mu tashi fa ƴanuwa, mu yi ta yin addu'a
 Mu yi shelar Yesu da cetonsa da ƙarfin zuciya.
 Korus</lyrics>
</song>